Isa ga babban shafi
Libya

Sojan Libya sun kai hare-hare sansanonin 'yan kungiyar

Dakarun Gwamnatin kasar Libya sunyi ta wutan bama-bamai wasu sansanoni na ‘yan kungiyar IS dake garin Sirte, inda ake ta kai  hare-hare ta sama, domin Soja su shiga garin ta kasa don kwace yankin daga hannun kungiyar. 

Sojan Libya a bakin daga
Sojan Libya a bakin daga REUTERS/Stringer
Talla

Reda Issa kakakin Gwamnatin Hadin Kai na Libya ya shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP cewa yau Alhamis sojan suka kai wannan hari.

Ya bayyana cewa Sojoji injiniyoyi na kokarin share nakiyoyi da aka daddasa a hanyoyin shiga garin na Sirte

Idan har akayi nasarar kwace garin Sirte daga hannun ‘yan kungiyar IS zai kasance babbar nasara ga Gwamnatin Libya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.