Isa ga babban shafi
Libya

Babbar mahakar mai za ta koma karkashin gwamnatin Libya

A cikin wata sanarwar bai daya da suka fitar a yau Laraba, Kasashen yammacin duniya 6 sun bukaci ganin kula da dukkanin cibiyoyin man fatur din kasar Libya ya koma karkashin kulawar gwamnatin hadaka ta kasar. 

Wani yankin Libiya dake fama da rikici
Wani yankin Libiya dake fama da rikici REUTERS/Stringer
Talla

Gwamnatocin kasashen Jamus, Amurka Faransa, Italiya da kuma Britaniya ne, suka bukaci mayar da daukacin kula da cibiyoyin hakar man fetur din kasar ta Libya ga hannun gwamnatin hadin kan kasar, sun kuma bukaci hakan ba tare da gindaya wani sharadi ko jan kafa ba.

Haka kuma sun bukaci daukacin bangarorin dake rike da makamai a kasar su kawo karshen tashe tashen hankula da kuma gujewa zagon kasa ko lalata gine ginen samar da makamashin man fetur din na kasar ta Libya

Dakarun dake biyayya ga janar Khalifa Haftar ne, dake da sansani a gabashin kasar ta Libiya da kuma ke adawa da gwamnatin hadin kan kasar, sun yi barazanar kai hari a Zueitina, domin karbe ikon kula da cibiyar hakar man fetur din kasar.

Zueitina daya ce daga cikin manyan mahakun man dake gabar gabashin kasar Libya kimanin kilomita 100 kudu maso yammacin birnin Bengazi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.