Isa ga babban shafi
Libya

Al'ummar Libya sun gaji da rikicin da kasar su ke fuskanta- MDD

Babbar mashawarciyar Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Libya ta yi ikirarin cewa al’ummar kasar sun gaji da rikicin da su ke fuskanta na fiye da shekaru 10 inda su ke shirye don shiga rumfunan zabe da nufin kada kuri’a a zaben kasar mai zuwa duk da sabon rikicin siyasar da ya barke.

Mataimakiyar Musamman ga Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya kan Harkokin Siyasa a Libya Stephanie Williams yayin halartar taron tattaunawa kan siyasar kasar a birnin Tunis, na kasar Tunisia Nuwamba 9, 2020.
Mataimakiyar Musamman ga Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya kan Harkokin Siyasa a Libya Stephanie Williams yayin halartar taron tattaunawa kan siyasar kasar a birnin Tunis, na kasar Tunisia Nuwamba 9, 2020. REUTERS - ZOUBEIR SOUISSI
Talla

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Faransa, babban mashawarcin MDD kan rikicin na Libya Stephanie Williams ta ce al’ummar Libya sun kosa da rikicin, ta yadda hatta ‘yan siyasar da ke rikici da juna ke fatan hada hannu don lalubo bakin zaren.

Dai dai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wutar bangarori masu rikici da juna a Libyan ke cika watanni 17 cike da fargabar yiwuwar wargajewarta musamman saboda rikicin siyasar baya bayan nan, Williams ta ce duk da hakan dubban al’ummat kasar a shirye suke su fita rumfunan zabe a kowannen lokaci daga yanzu don samar da zaman lafiya a kasar.

A watan Disamban bara ne aka tsara gudanar da zaben Libya karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya amma kuma rikice-rikicen siyasa masu alaka da rashin tantance wasu ‘yan takara baya ga kararrakin da ke gaban kotuna ya tilasta dage zaben wanda har zuwa yanzu ba a kai ga sanar da lokacin gudanar da shi ba.

Wannan mataki na dage zabe ya karya gwiwar ‘yan libya mutum miliyan biyu da dubu dari 8 tuni suka yi rijista don kada kuri’a a zaben duk da yadda tsagaita wutar watan Oktoba ta basu kwarin gwiwar yiyuwar gudanar da zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.