Isa ga babban shafi
Libya

Majalisar dokokin Libya na ganawa da 'yan takaran Firaminista

Majalisar Dokokin Libya ta fara zama na musamman domin zabo wanda zai maye gurbin Firaminista Abdulhamid Dbeibah da ya sauka a mukamin sa domin tsayawa takarar shugaban kasa.

Jagoran gwamnatin Libya da ya sauka don takarar firaminitsa Abdel Hamid Dbeibah.
Jagoran gwamnatin Libya da ya sauka don takarar firaminitsa Abdel Hamid Dbeibah. via REUTERS - POOL
Talla

Firaminista mai barin gado Abdulhamid Dbeibah ya karbi iko ne shekara guda da ta gabata, domin jagorancin gwamnatin rikon kwarya kafin gudanar da zaben da aka shirya yi a watan Disambar bara.

Sakamakon dage zaben da aka yi na har sai illa masha Allahu saboda shari’ar da ake a gaban kotu da kuma rashin halartsr wasu ‘yan takara, shugaban majalisar dokoki Aguilla Saleh ya kaddamar da shirin samo wanda zai karbi ragamar tafiyar da kasar a matsayin Firaminista.

Ana sa ran majalisar ta kada kuri’a tsakanin tsohon ministan cikin gida Fathi Bashaga da Khaled al-Bibass a ranar Alhamis mai zuwa.

Kasar Libya ta fada cikin tashin hankali tun daga shekarar 2011 bayan hallaka shugaba Muammar Ghadafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.