Libya ta jinkirta wallafa sunayen 'yan takarar zaben shugabancin Libya
Hukumar zaben kasar Libiya ta jinkirta fitar da jerin sunayen 'yan takarar zaben shugabancin kasar da aka shirya zai gudana cikin kasa da makwanni biyu.
Wallafawa ranar:
Kawo yanzu dai babu karin bayani akan dalilan da suka sanya hukumar zaben Libiyar daukar matakin ba, zalika ba ta bayyana sabuwar ranar da zaben zai gudana ba.
Sai dai wasu masu bibiyar lamurran kasar sun ce hakan ba zai rasa nasaba da cewar a karkashin doka zagayen farko na zaben shugaban kasar ba zai yiwu ba a ranar 24 ga watan Disamba saboda 'yan takara na da damar yin yakin neman zabe na tsawon makwanni biyu bayan fitar da jerin sunayen da aka tantance.
A ranar 2 ga watan Disamba wata kotu a Libya ta mayar da dan marigayi Moamer Kadhafi, Seif al-Islam Kadhafi, cikin ‘yan takara bayan soke sunansa da hukumar zabe ta yi a baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu