Isa ga babban shafi
Libya-MDD

Jami'an MDD za su ci gaba da zama a Libya duk da dakatar da aikinsu

Kwana guda bayan jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun sanar da dakatar da aikinsu a Libya jagoran shirin ya shaidawa kwamitin tsaro na majalisar cewa za su ci gaba da zama a kasar har zuwa kammala zaben watan gobe.

Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Libya Jan Kubis.
Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Libya Jan Kubis. STR AFP/File
Talla

A wata zantawarsa da jami’an kwamitin tsaron a Libya, Jan Kubis ya ce tun a ranar 17 ga watan nan ya mika takardar ajje aikinsa ga Sakatare Janar na Majalisar Antonio Guterres.

Sai talatar nan ne dai Majalisar Dinkin Duniyar ta amince da ajje aikin Jan Kubis wadda matakin ajjewar a hukumance zai fara aiki daga ranar 10 ga watan Disamba, sai dai jami’in ya ce zai ci gaba da zaman a Libyan har zuwa kammala zaben kasar.

Jami’an majalisar 15 da ke karkashin Jan Kubis a Libyan sun ce har yanzu basu da masaniya kan dalilin jagoran nasu na ajje aikin.

Jan Kubis dan Slovenia mai shekaru 69 ya ce zai zauna a Libya har zuwa watan Disamba kamar yadda ya tabbatarwa da Majalisar Dinkin Duniya.

Zaben Libyan na ranar 24 ga watan Disamba ana fatan ya kawo karshen yakin shekaru 10 da kasar ta gani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.