Isa ga babban shafi
ZABEN-LIBYA

'Yan takara 61 ke neman shugabancin Libya

Hukumar zaben kasar Libya tace mutane 61 suka gabatar da takardun su na neman tsayawa takarar zaben shugaban kasar da za’a gudanar a ranar 24 ga watan Disamba mai zuwa.

Firaministan rikon kwarya Abdelhamid Dbeibah
Firaministan rikon kwarya Abdelhamid Dbeibah © Mahmud TURKIA / AFP
Talla

Hukumar tace daga cikin wadanda suka gabatar da takardun su kafin rufe karbar takarar yammacin litinin, akwai Firaminista Abdelhamid Dbeiba da shugaban majalisar dokoki Aguila Salah da Fathi Bashagha, tsohon minista a gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Sauran fitattun ‘Yan takarar sun hada da Janar Khalifa Haftar da ya dade yana yaki domin kwace ragamar jagorancin Libya da kuma Seif al-Islam Ghadafi, wanda ‘da ne ga tsohon shugaban kasa Muammar Ghadi.

Janar Khalifa Haftar
Janar Khalifa Haftar - LIBYA ALHADATH TV/AFP

Masu gabatar da kara na soji sun bukaci hukumar zaben da ta dakatar da tantance Janar Haftar da Seif al Islam har sai sun amsa tuhumar da ake musu.

Janar Haftar na fuskantar tuhumar laifuffukan yaki a kasar Amurka, yayin da kotun hukunta manyan laifuffuka ke neman Ghadafi tun daga shekarar 2011 saboda cin zarafin Bil Adama da kuma laifuffukan yaki.

Seif al-Islam Kadhafi
Seif al-Islam Kadhafi STRINGER libyan High National Electoral Comission FB Page/AFP/File

Ana saran gudanar da zaben shugaban kasar ne a ranar 24 ga watan Disamba mai zuwa.

Tun bayan kashe shugaba Muammar Ghadafi a shekarar 2011, kasar Libya ta fada cikin tashin hankalin da yayi sanadiyar rasa dubban rayuka, yayin da kasar ta zama dandalin Yan bindiga da masu aikata laifuffuka, ciki harda cinikin mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.