Isa ga babban shafi
RIKICIN-LIBYA

Macron ya bukaci Rasha da Turkiya da su janye sojojin hayar dake Libya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci kasashen Rasha da Turkiya da su gaggauta janye sojojin hayar kasashen su dake cikin Libya domin bada damar gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘Yan majalisu.

Shugaba Emmanuel Macron
Shugaba Emmanuel Macron © Nigeria presidency
Talla

Yayin da yake jawabi wajen taron kasashen duniya da aka gudanar yau a Paris akan halin da Libya ke ciki da kuma shirin zaben kasar mai zuwa, Macron yace ya zama dole a aiwatar da shirin janye sojojin hayar kasashen waje dake cikin Libya.

Shugaba Macron ya yaba da rahotan cewar sojojin haya 300 dake taimakawa Janar Khalifa Haftar yaki zasu fice daga Libya cikin kasar a matakin farko.

Rahotanni sun ce akwai dubban sojojin haya daga kasashe da dama wadanda bangarorin dake kokawar mulki a Libya suka dauko domin taimaka musu kwace iko.

Kasar Libya ta fada cikin tashin hankali tun bayan kawar da tsohon shugaban kasa Muammar Ghadafi daga karagar mulki, sakamakon juyin juya halin da ya mamaye kasashen Larabawa, abinda yayi sanadiyar kashe shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.