Isa ga babban shafi
Libya-Zabe

Firaminista Dbeiba ya shiga jerin 'yan takarar neman shugabancin Libya

Firaministan rikon kwaryar Libya Abdulhamid Dbeibah ya yi rajistar shiga takarar zaben shugaban kasar da za a yi a watan gobe, abinda ya sa shi cikin jerin yan takarar da suka hada da ‘dan tsohon shugaban kasa Moammar Ghadafi, wato Seil al-Islam.

Firaministan Libyan Abdel Hamid Dbeibah.
Firaministan Libyan Abdel Hamid Dbeibah. AP - Hazem Ahmed
Talla

Firaministan Abdulhamid Dbeibah ya sanya hannu akan takardun tsayawa takarar sa ne a ofishin hukumar zabe dake birnin Tripoli, kwana guda kafin cikar wa’adin tsayar da ‚yan takara.

Dbeibah mai shekaru 62 da ya fito ne daga yankin Misrata, ya zama firaministan rikon kwarya ne a watan Fabarairu domin shirya zaben kasar.

A ranar 24 ga watan Disamba mai zuwa ake saran gudanar da zaben shugaban kasar Libya, a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke kokarin kawo karshen tashin hankalin da ya mamaye kasar tun bayan kashe shugaba Moammar Ghadafi a shekarar 2011.

Daga cikin ‘Yan takarar shugaban kasar guda 4 akwai shugaban majalisar dokoki Aguila Saleh da Janar Khalifa Haftar da kuma ‘dan tsohon shugaban kasa Ghadafi, Seif al Islam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.