Isa ga babban shafi
ZABEN LIBYA

Hukumar zaben Libya ta soke takarar Seif al-Islam da wasu mutane 24

Hukumar zabe a kasar Libya tayi watsi da takarar zaben shugaban kasar Seif al-Islam Ghadafi wanda ‘da ne ga tsohon shugaban kasa Muammar Ghadafi.

Seif al Islam Ghadafi
Seif al Islam Ghadafi -, Mahmud Turkia AFP/Archivos
Talla

Hukumar tace Seif al-Islam na daya daga cikin ‘Yan takara 25 da taki amincewa da takardun takarar su a zaben da za’ayi a ranar 24 ga watan Disamba.

Daga cikin wadanda suka gabatar da takardun takarar akwai Janar Khalifa Haftar wanda ya dade yana yaki domin karbe ikon kasar, yayin da kotu a Amurka ke neman sa ruwa ajallo domin fuskantar tuhumar laifffukan yaki.

Sauran ‘Yan takarar sun hada da Firaministan rikon kwarya Abdelhamid Dbeiba da shugaban majalisar dokoki da kuma tsohon ministan cikin gida Fathi Bashagha.

Janar Khalifa Haftar
Janar Khalifa Haftar - LIBYA ALHADATH TV/AFP

Mata biyu ne kacal suka gabatar da takardun su na yin takara, kuma sun hada da Laila Ben Khalifa mai shekaru 46 da Hunayda al-Mahdi.

Shugaban hukumar zaben kasar Imad al-Sayed yace mutane 98 suka gabatar da takardun tsayawa takarar zaben shugaban kasar.

‘Yan kasar Libya miliyan 2 da dubu 800 suka yi rajistar kada kuri’a, kuma ya zuwa yanzu miliyan guda da dubu 700 sun karbi katin zaben su.

Kasar Libya ta fada cikin tashin hankali tun bayan kashe tsohon shugaban kasa Muammar Ghadafi sakamakon zanga zangar juyin juya halin da ta mamaye kasashen Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.