Isa ga babban shafi

Kasashen Nijar, Benin da Togo sun gaza biyan Najeriya Naira biliyan 5 na lantarkin

Hukumar da ke kula da lantarki a Najeriya ta ce kasashen Nijar da Benin da kuma Togo sun gaza biyan bashin Naira biliyan 5 da miliyan 86 na kudin lantarkin da ake binsu ba, cikin jumullar kudin lantarkin da suka sha a shekarar 2020 na Naira biliyan 16 da miliyan 31.

Kamfanin samar da hasken wutar lantarki na Najeriya
Kamfanin samar da hasken wutar lantarki na Najeriya Daily Trsut
Talla

Cikin rahoton yadda hada-hadar lantarki ta gudana a 2020 da hukumar ta NERC a Najeriya ta fitar ta ce kamfanonin lantarkin kasashen 3 da suka kunshi SNE a Nijar da SBEE a Benin da CEET a Togo sun gaza biyan kudin a tsawon lokacin da aka dauka daga mika musu takardun bashin zuwa yanzu.

Rahoton na NERC, ya ruwaito hukumar na cewa bayan damkawa kasashen 3 takardun wutar da aka basu a shekarar ta 2020 Naira biliyan 10 da miliyan 45 kadai suka iya biya yayinda ake binsu bashin Naira biliyan 5 da miliyan 86.

Rahoton ya ci gaba da cewa baya ga kasashen 3 hatta kamfanin karafa na Ajaokuta ya gaza biyan ko sisi daga jumullar Naira biliyan 1 da miliyan 8 na lantarkin da ya sha a shekarar.

NERC ta sanar da shirin soke lasisin wasu kamfanonin lantarki da suka gaza biyan bashin da ake binsu yayinda za ta kara karfin lantarkin da ta ke samarwa da megawatts 667.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.