Isa ga babban shafi

Yajin aikin ma'aikatan lantarki: Wuta ta dauke dif a fadin Najeriya

A Najeriya yanzu haka wasu sassan ƙasar da dama na cikin duhu sakamakon yajin aikin da ma'aikatan wutar lantarkin ƙasar suka fara.

Karo na shida kenan da ake samun daukewar lantarki a fadin kasar cikin shekara guda a Najeriya
Karo na shida kenan da ake samun daukewar lantarki a fadin kasar cikin shekara guda a Najeriya AFP/File
Talla

Manyan cibioyoyin kamfanin dillancin wutar lantarkin na kasar sun sanar da cewa za su katse na'urorin da ke bayar da hasken lantarki a Abuja, babban birnin ƙasar da kuma Lagos ranar Laraba.

Yajin aikin ya samo asali ne saboda rashin jituwar da aka samu tsakanin Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma'aikatan Lantarkin da kuma Kamfanin Dillancin Lantarki na Najeriyar.

Kungiyar ma'aikatan na lantarki ta ce ta na son gwamnatin kasar mutunta yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2019, ciki kuwa har da batun biyan tsoffin ma'aikata da suka yi aiki karkashin tsohon kamfanin lantarki hakkokinsu.

Karo na shida kenan da ake samun daukewar lantarki a fadin kasar cikin shekara guda a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.