Isa ga babban shafi

'Yan ta'addan Sahel na karkata hare-harensu zuwa gabar tekun Afrika- Bincike

Matsalolin tsaro masu alaka da hare-haren ta’addancin kungiyoyi masu ikirarin jihadi na fadada a nahiyar Afrika, inda cikin shekaru 10 da suka gabata ayyuka irin wadannan suka fantsama daga yankin Sahel zuwa kasashen yammacin Afrika da ke gabar teku.

Wani yanki na Menaka a Mali da ke fama da hare-haren 'yan ta'adda.
Wani yanki na Menaka a Mali da ke fama da hare-haren 'yan ta'adda. © AFP PHOTO / Etat Major des Armees
Talla

Wani bincike da kamfanin dillancin labaran Faransa ya gudanar, ya gano yadda ‘yan ta’adda suka fadada hare-harensu daga arewaci da tsakiyar Mali da suka faro a shekarar 2012 zuwa makwabtan kasar da suka kunshi Burkina Faso da jamhuriyar Nijar.

Alkaluman na AFP ya ce, bayan fantsamuwar hare-haren ‘yan ta’addan zuwa kasashen Sahel yanzu akwai fargabar hare-haren na tsallakawa kasashen gabar teku, inda tuni aka fara ganin take-taken tasowar wasu kungiyoyi tsageru bisa ikirarin jihadi.

Bayan faruwar wasu hare-hare a arewacin kasashen Benin da Ivory Coast da kuma Togo tuni gwamnatocin kasashen 3 suka daura damarar tunkarar matsalolin tsaron da ke shirin afkawa kasashen.

Hafsoshin tsaron kasashen 3 a wani taro da suka gudanar sun yi zubeben kwarya kan matsalolin tsaron da suka addabi makwabtansu kasashen yankin Sahel don lalubo bakin ta inda za su magance tasu matsalar.

Bayan da Sojoji suka yi juyin mulki a Mali cikin watan Agustan 2020 tare da katse alaka da Faransa wadda ke taimakwa kasar a yaki da ta’addanci, kaso mai yaw ana mayakan da ke kaddamar da hare-hare a kasar sun fadada ayyukan ta’addancinsu zuwa makwabta.

Ko a watan jiya shugaba Patrice Talon na Benin ya shaidawa shugaban Faransa Emmanuel Macron cewa kasar na bukatar agajin kayakin yaki musamman jirage marasa matuka don lalubo maboyar ‘yan ta’addan tare da kakkabe su.

Cikin kasashen gabar tekun, Benin ce wadda ta fi fuskantar barazanar hare-haren ‘yan ta’addan yayinda Ivory Coast da Togo suka sanar da daura damarar kakkabe masu tsattsauran ra’ayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.