Isa ga babban shafi

Mali ta ce za ta janye daga kungiyar G5 Sahel daga 30 ga Yuni

Wata guda bayan da Mali ta ce za ta janye daga kawancen kungiyar kasashen Sahel, gwamnatin mulkin sojin kasar ta sanar da cewa janyewar za ta fara aiki daga ranar 30 ga watan Yunin nan.

Shugaban Mali Assimi Goita.
Shugaban Mali Assimi Goita. AP
Talla

Daga wannan rana ce dakarun Mali da ke  cikin hadakar yaki da ta’addanci a gabashi da tsakiyar kasar, da kuma jami’an sojin Mali da ke aiki a shelkwatar rundunar hadakar za su janye kacokan.

An kafa rundunar yaki da ta’addancin ta yammacin Afrika ne a shekarar 2014 da goyon bayan Faransa, kuma ta kunshi Mauritania, Chadi, Burkina Faso da Nijar.

Dakarun G5 Sahel din na aiki ne a yankuna 3 da suka hada da iyakar Mali da Mauritania, da iyakar Chadi da Nijar da kuma tsakiya da ta hade yakunan kan iyakokin 3.

Mali ta yanke shawarar janyewa daga wannan hadaka ce bayan da aka hana ta shugabantar kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.