Isa ga babban shafi
Boko Haram

Bazoum ya nemi taimakon Buhari kan yaki da 'yan ta'adda a Sahel

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya bukaci Najeriya da ta taimaka wajen kafa wata sabuwar rundunar sojin hadin kai wadda za ta yi yaki da ‘Yan ta’addan da suka addabi kasashen da ke yankin Sahel.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohamed tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © nigeria presidency
Talla

Wannan ya biyo bayan rawar da Najeriya ta taka wajen kafa rundunar sojin hadin kai ta MJTF da ke yaki da mayakan Boko Haram a Yankin Tafkin Chadi wanda ya samu gudumawar sojoji daga Najeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru.

Shugaba Bazoum wanda ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Abuja dangane da bukatar, ya ce ana bukatar irin wannan runduna a Yankin Sahel domin fuskantar kalubalen ‘Yan ta’adda wadanda suke kashe rayukan jama’a ba tare da kaukautawa ba.

Bazoum ya ce ganin nasarar da ake samu wajen yaki da mayakan Boko Haram a Tafkin Chadi, ana bukatar irin wannan rundunar matuka wadda za ta fuskanci kalubalen tsaron a Yankin Sahel gaba daya.

Shugaban ya ce Najeriya a matsayinta na babbar kasa kuma mai karfin tattalin arziki, tana da rawar da zat a taka sosai wajen kafa irin wannan runduna ta soji da kuma rage nauyin kudin aikin da zata yi domin yakar ‘Yan bindigar.

Yanzu haka Jamhuriyar Nijar na kokarin tattaunawa da wasu kungiyoyin 'Yan ta’addan da hare harensu ya daidaita yankin kudu maso yammacin kasar, yayin da ake fargabar karuwar tashin hankalin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.