Isa ga babban shafi

Akwai kusanci tsakanin Mayakan jihadi a Sahel da ISWAP- Faransa

Yayin da rundunar sojin Faransa da ke fada da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel wato Barkhane ke daf da kammala aikin janye dakarunta daga Mali, yanzu haka rundunar na ci gaba da sauya salo ta hanyar rage yawan dakarunta da ke zuwa fagen daga, inda a maimakon haka za su mayar da hankali wajen taimaka wa dakarun kasashen Afirka irinsu jamhuriyar Nijar.

Shugaban tsagin kungiyar Boko Haram ISWAP da ke biyayya ga kungiyar IS Abu Musab Al-Barnawi
Shugaban tsagin kungiyar Boko Haram ISWAP da ke biyayya ga kungiyar IS Abu Musab Al-Barnawi Guardian Nigeria
Talla

Kakakin rundunar sojin Faransa Janar Pascal Ianni, ya bayyana wa Timbi Bah na sashen RFI/Fulfulde yadda suke kallon ayyukan kungiyar Boko Haram wadda ga alama ke neman samun kusanci da sauran kungiyoyin ta’addanci da ke Burkina Faso, Mali da kuma Jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.