Isa ga babban shafi

Nijar za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaro a Sahel

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya sha alwashin taimakawa kwamitin da kungiyar ECOWAS ta kafa domin lalubo hanyar magance matsalar tsaron da ta addabi wasu kasashen yankin a karkashin tsohon shugaban kasa Mahamadou Issofou.

Shugaban Nijar Bazoum Muhammad da tsohon shugaban kasar Issoufou Muhammadu a fadar shugaban kasar.
Shugaban Nijar Bazoum Muhammad da tsohon shugaban kasar Issoufou Muhammadu a fadar shugaban kasar. © Niger presidency
Talla

Bazoum ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi jagorancin kwamitin wanda ya kunshi wakilan Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka ta AU da kungiyar G5 Sahel a fadar sa dake Birnin Yamai.

Shugaba Issofou ya shaidawa Bazoum cewar kafa wannan kwamiti ya biyo bayan sanarwar da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayi lokacin da ya ziyarci Yamai makwannin da suka gabata, inda ya sanar da shi a matsayin wanda zai jagoranci wannan kwamiti mai matukar muhimmanci wajen samo hanyar zaman lafiya a Yankin.

Issofou yace wannan ne lokacin da zasu gudanar da taron kwamitin na farko, abinda ya sa suka ziyarci shugaba Bazoum domin tattaunawa da shi akan ayyukan dake gaban su da suka hada da matsalar tsaron Sahel da sauyin yanayi da ayyukan jinkai da yawan jama’a da tattalin arziki da kuma kayan more rayuwa.

Tsohon shugaban kasar ya kuma ce sun yi amfani da ganawar wajen daukar shawarwari daga shugaba Bazoum musamman dangane da hanyoyin da ya dace su bi wajen samun nasarar sauke nauyin dake kan su.

Issofou yace shugaba Bazoum yayi alkwarin taimaka musu wajen samun nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.