Isa ga babban shafi

Kotun Gambia ta yanke hukuncin kisa kan tsoffin jami'an Jammeh

Kotu a Gambia ta yanke hukuncin kisa kan wasu tsoffin jami’an leken asiri guda biyar bisa samun su da laifin kashe wani dan siyasa a zamanin mulkin tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh.

Ana zargin Jammeh da aikarta laifuka da dama a yayin shugabancin kasar Gambia.
Ana zargin Jammeh da aikarta laifuka da dama a yayin shugabancin kasar Gambia. AFP - MARCO LONGARI
Talla

Alkalin babbar kotun Kumba Sillah-Camara ta yanke hukuncin ne kan kashe Ebrima Solo Sandeng, wani jigo a jam'iyyar adawa ta UDP.

Babbar kotun birnin Banjul din ta yanke wa tsohon shugaban gudanarwa na Hukumar Leken Asirin Kasar, Sheikh Omar Jeng, da wasu jami’an hukumar, Babucarr Sallah, Lamin Darboe da Tamba Mansary, hukuncin kisa bayan samun su da laifi a kan wannan zargi da ake musu.

Haruna Susso, shi ma wani jami’in Hukumar Leken Asirin kasar, da Lamin Sanyang, wanda jami’in jinya ne, an same su da laifin kisa da kuma haddasa rauni.

An kama Sandeng a lokacin wata zanga-zangar adawa da Jammeh a watan Afrilun shekarar 2016, ya kuma rasu a gidan yari bayan kwana biyu, sakamakon duka da azabtarwa.

Mutuwar Sandeng ce, ta janyo kafa wata kungiyar siyasa, wadda ta haddasa tumbuke shugaba Yahya Jammeh, wanda ya jagoranci kasar tsawon shekaru 22.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.