Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kashe sama da fararen hula 100 a Mali

Gwamnatin Mali tace Fiye da fararen hula 130 ne aka kashe a wasu garuruwa biyu dake tsakiyar kasar, a wasu hare-haren da ake zargin mayakan masu ikirarin jihadi ne, suka kai a karshen mako.

Wani sojin Mali cikin mota a yankin Mofti a shekarar 2020.
Wani sojin Mali cikin mota a yankin Mofti a shekarar 2020. © MICHELE CATTANI/AFP
Talla

Sanarwar gwamnatin Mali na wannan Litinin ta daura alhakin kisan fararen hula 132 kan mayakan Macina Katiba da ke da alaka da Al-Qaeda, bayan da suka kai wasu jerin hare-hare daren Asabar a kauyukan Dillassagou da wasu yankuna biyu na yankin tsakiyar kasar.

Wani zababben jami'in yankin da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa ko a wannan Litinin an ci gaba tashin hankalin.

Adadin na iya zarta haka

Yayin da wani jami'in na daban mai suna Nouhoum Togo da ya ce sojoji sun isa wurin da aka kai harin, inda suka tattara gawarwakin wadanda suka mutu, yace adadin na iya zarta 100.

Tun a shekarar 2012 ne kasar Mali ke fama da tashe tashen hankula daga kungiyoyi da ke da alaka da Al-Qaeda da kuma IS, lamarin da ya jefa kasar cikin rikici.

Rikicin da ya faro a arewacin kasar ya bazu zuwa tsakiyar kasar da kuma makwabtan Burkina Faso da Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.