Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun kashe fararen hula 20 a Mali

 ‘Yan bindiga sun kashe akalla fararen hula 20 a yankuna daban daban na garin Gao da ke Arewacin Mali wanda ke fuskantar rikice-rikice, kamar yadda jami’an ‘yan sanda da kuma hukumomin yankin suka shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Dakarun Mali da ke sintiri a yankin Gao.
Dakarun Mali da ke sintiri a yankin Gao. © AFP/Souleymane Ag Anara
Talla

Wani jami’in dan sanda a Bamako wanda ya nemi a sakaye sunan sa ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa an kashe akalla mutane 20 a Ebak da ke da nisan kilo mita 35 daga Gao.

Sai dai babu wata majiya da ta tabbatar da cewar masu ikirarin jihadi ne suka kai harin.

Yankin Gao na fuskantar kalubalen tsaro tun bayan fara rikicin a shekarar 2012, a lokacin da ‘yan tawayen yankin suka tashi tsaye kan Bamako.

A shekarar 2015, sun sanya hannu a kan yarjejeniyar samar da zaman lafiya a tsakanin su, sai dai har yanzu ba’a kaddamar da ita ba.

A yanzu dai kungiyoyin masu ikirarin jihadi da ke da alaka da kungiyar Al-Qaeda da kuma IS na ci gaba da kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati da wadanda ke goya mata baya da ma su kansu a kokarin kwace iko.

A wani rahoto na baya-bayan nan da sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya fitar, ya ce yankin Gao da kuma Menaka na fuskantar kalubalen tsaro da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.