Nakiya ta kashe wani sojin Majalisar Dinkin Duniya a Mali
Wani jami’in rundunar kiyaye zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya ya mutu bayan da ya taka nakiya a arewacin Mali da ke fama da rikici a yau Lahadi, a yayin da yake sintiri a yankin, kamar yadda shugaban rundunar ta MINUSMA a Mali ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Wallafawa ranar:
Jami’in kiyaye zaman lafiyar wanda yake daga cikin tawagar sojin kasar Guinea da ke aiki da dakaru na musamman ya ji rauni ne da farko, daga bisani ya mutu a asibiti a garin Kidal.
Wanann hatsari na zuwa ne a daidai lokacin da ake tattaunawa mai cike da tankiya a kan sabanta zaman rundunar ta MINUSMA a Mali.
Jimillar dakarun kiyaye zaman lafiya na rundunar MINUSMA 175 ne suka mutu sakamkon rikicin da ake a Mali.
Rikicinn Mali ya yi sanadin mutuwar dubban daruruwan mutane, tare da daidaita da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu