Isa ga babban shafi

Gwamnatin Zimbabwe ta musanta fataucin sassan jikin dan Adam daga yan kasar

A  Zimbabwe,musamman a babban birnin kasar Harare, wani al’amari da ya ja hankali jama’a shine ta yada  aka ga wasu daga cikin yan kasar na nuna yatsun kafafuwansu don kawo karshen jita-jita da ake yadawa na cewa wasu daga cikin yan kasar sun sayar da sassan jikin su  don magance matsalar talauci da suke fuskanta.

Takardun kudi na kasashen Duniya
Takardun kudi na kasashen Duniya © REUTERS/Kacper Pempel/Illustration
Talla

Tsawon wannan makon, hukumomin kasar ta Zimbabwe da matsakaicin talauci ya mammaye suke ta kokarin ganin sun karyata wannan jita-jita na cewa wasu daga cikin yan kasar na sayar da sassan jikinsu  ga matsafa musaman  yatsu,inda wasu rahotanni ke nuni cewa ana sayar da yatsa daya a kan kudi  dala dubu 20 zuwa dubu 40.

Tun bayan mutuwar tsohon Shugaban kasar Robert Mugabe,tattalin arzikin kasar ya fada yanayi marar kyau,ga tsadar rayuwa,jama'a na fuskantar datsewar kayakin more rayuwa.

Mataimakin Ministan yada labaren kasar  Kindness Paradza ya musanta wannan labara,da cewa babu wani abun mai kama da haka dake faruwa a Zimbabwe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.