Zimbabwe ta ayyana dokar hana zirga-zirga saboda Korona
Gwamantin Zimbabwe daga jiya asabar ta aiwatar da dokar hana zirga-zirgar jama’ar bayan da aka fuskanci yawaitar masu kamuwa da cutar Coronavirus.
Wallafawa ranar:
A wannan sabuwar dokar gwamnatin kasar na bukatar mutane su takaita yawan masu halartar jana’izza, banda haka ,hukumomin sun haramta taruruka na aure, biki, taruruka a mujami’u, gidajen cin abinci, gidajen rawa na tsawon wata daya.
Mataimakin Shugaban kasar dake da mukamin Ministan kiwon lafiyar kasar Zimbabwe ne ya fitar da wannan sanarwa.
A yanzu haka kasar na da kusan mutane 14.084 da suka kamu da kwayar cutar,yayinda 369 suka mutu a kasar ta Zimbabwe,kasar da tattalin arzikin ta ya kama hanyar rushewa tun farkon shekara ta 2000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu