Zimbabwe na fama da karancin cimaka -WFO
Hukumar abinci ta Duniya (WFO) na kokarin samar da kusan milyan 200 na dalla,kudadden da hukumar za ta yi amfani da su wajen kai dauki cikin gaggawa ga yankunan karkara na kasar Zimbabwe dake fama da karancin cimaka.
Wallafawa ranar:
An share shekaru wadanan yankuna na fuskantar fari da karancin ruwan sama.
Hukumar ta fitar da wasu alkaluma dake nuna cewa kusan mutane milyan daya ne suka karu ga wandada ke bukatar agajin gaggawa musaman amfana da abinci mai gina jiki a kasar ta Zimbabwe.
Wasu kasashen Afrika musaman na yankunan Sahel na daga cikin yankunan da matsallar tsaro ta tilasatawa manoma da dama dakatar da ayukan su,lamarain da ya haifar da karancin cimaka a wadanan wurrare a cewa hukumar abinci ta Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu