Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Likitocin Zimbabwe sun ki amsa bukatar komawa bakin aiki

Jami’an lafiyar kasar Zimbabwe da suka fuskanci dakatarwa biyo bayan yajin aiki sakamakon rashin biyansu albashi, sun yi watsi da bukatar gwamnati ta neman su sake komawa bakin aiki.

Likitocin Zimbabwe da suka bijirewa komawa bakin aiki bisa bukatar gwamnati.
Likitocin Zimbabwe da suka bijirewa komawa bakin aiki bisa bukatar gwamnati. REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Cikin sanarwar da kungiyar likitocin kasar ta fitar a jiya Juma’a ta ce baza su amsa bukatar gwamnati ta komawa bakin aiki ba, har sai anyi zama na musamman ba basu cikakkun hakkokinsu kamar kowanne ma’aikata.

Tun a ranar 3 ga watan Satumba ne jami’an lafiyar suka tsunduma yajin aiki sakamakon rashin biyansu wadataccen albashin da ya gaza dala 100 a kowanne wata, matakin da ya harzuka gwamnati tare da sallamarsu daga bakin aiki.

Gwamnatin Zimbabwe dai ta baiwa korarrun likitocin zabin komawa bakin aiki nan da sa'o'i 48 ko kuma ci gaba da fuskantar kora har abada.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.