Isa ga babban shafi
Mali

'Yan ta'adda sun kashe mutane kusan 40 a arewacin Mali

Gungun mayakan 'yan ta'adda da ke da alaka da kungiyar IS sun kashe mutane kusan 40 cikin makon nan yankin arewacin kasar Mali, inda a yanzu haka ke fama da rikici tsakanin kungiyoyin mayaka masu ikirarin jihadi da ke gaba da juna.

Wasu sojojin kasar Mali yayin aikin Sintiri.
Wasu sojojin kasar Mali yayin aikin Sintiri. AFP/Philippe Desmazes
Talla

Wasu majiyoyi sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar dukkanin wadanda ‘yan ta’addan suka kashe fararen hula ne a wurare daban-daban guda uku a yankin Tessit da ke kusa da kan iyakar Burkina Faso da Nijar.

Wani jami’i da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, ya ce har yanzu adadin wadanda ‘yan ta’addan suka kashe na wucin gadi ne saboda rashin cikakkun bayanai kan farmakin daga yankin na Tessit mai nisa da kuma hatsari.

Bayanai daga yankin na arewacin Mali dai sun ce tun shekarar 2020 kungiyoyin mayakan na ‘yan ta’adda masu gaba da juna ke gwabza fada a tsakaninsu, baya ga kaiwa sojojin kasar ta Mali da na kasashen ketare hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.