Isa ga babban shafi
Mali - Ta'addanci

Sojojin Mali 15 sun mutu sakamakon harin ta'addanci a tsakiyar kasar

Wani harin ta’addancin da masu ikirarin jihadi suka kai a kasar Mali ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar 15 tare da jikkata wasu guda 34.

Wasu sojojin Mali suna sintiri a tsakiyar kasar.
Wasu sojojin Mali suna sintiri a tsakiyar kasar. PHILIPPE DESMAZES / AFP
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 10 cikin guda 34 da suka jikkata na cikin hali rai kwakwai mutu kwakwai, sakamakon bam din da ‘yan ta’addan suka jefa musu bayan barin wuta da suka rika yi wa kwambar motocin su.

Wannan hari dai ya faru ne gab da kauyen Douentza da ke gundumar Mopti mai nisan kilomita 600 zuwa babban birnin kasar Bamako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.