Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

Mali ta bukaci ficewar dakarun Faransa cikin gaggawa sabanin watanni 6

Gwamnatin Sojin Mali ta bukaci gaggauta ficewar dakarun Faransa daga kasar ba tare da jinkiri ba matakin da ke zuwa bayan Paris ta sanar da shirin janye dakarunta daga kasar ta yankin Sahel amma a wani wa’adi na watanni a nan gaba.

Dakarun Faransa da suka fara ficewa daga Mali.
Dakarun Faransa da suka fara ficewa daga Mali. AP
Talla

Sanarwar kakakin gwamnatin ta Mali da gidajen talabijin din kasar suka karanta ta kai tsaye ga al’umma, ta bayyana rashin gamsuwa da aikin yaki da ta’addancin da Faransa ke ikirarin yi a kasar.

A cewar sanarwar shugabancin Mali bai amince da fitar dakarun Faransa nan da wani dadadden lokaci ba, abin da ya ke bukata shi ne ficewar dakarun cikin gaggawa ba tare da jinkiri ba.

A jiya Alhamis ne shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar da shirin kasar na janye dakarunta daga Malin don kawo karshen yakar ta’addanci a yankin na Sahel.

Acewar Macron dakarun za su fice daga Mali a daki daki na tsawon wani lokaci gabanin kammala ficewa daga kasar na akalla watanni 6 nan gaba.

Sanarwar ta Mali ta zargi Faransa da karya yarjejeniyar da tun farko ta sanya fara aikin dakarun a Mali tun a shekarar 2013 matakin da ya lalata dangantakar kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.