Isa ga babban shafi
Burkina Faso

'Yan ta'adda sun kashe mutane 41 a Burkina Faso

Gwamnatin Burkina Faso ta ayyana kwanaki biyu na zaman makoki na tsawon kwanaki biyu tun daga Lahadin nan, bayan da gungun ‘yan ta’adda masu ikirarin Jihadi suka kashe mutane akalla 41, a wani hari da suka kai a arewacin kasar mai fama da rikici.

Taswirar kasar Burkina Faso.
Taswirar kasar Burkina Faso. © RFI
Talla

Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar da yammacin ranar Asabar din da ta gabata, ta ce tawagar masu binciken da ta tura ne suka gano gawarwakin mutanen 41 da ‘yan ta’addan suka yi wa kwanton bauna.

Gwamnati ta ce wadanda suka mutun sun hada da jami’an rundunar jami’an tsaron sa kai, wadanda aka fi sani da dakarun VDP, wadanda aka kafa domin tallafawa sojojin Burkina Faso wajen yaki da ‘yan ta’adda.

Jami’an tsaron sa kan na VDP dai na samun horon tsawon kwanaki 14 ne kafin tura su aikin sinitiri dauke da kananan makamai a yankunan, Burkina Faso masu fama da matsalar tsaro.

Sanarwar gwamnati ta ce daga cikin wadanda harin na ranar Alhamis ya rutsa da su har da Ladji Yoro, jagoran masu tsaron sa kan na VDP, inda ta kara da cewar, har yanzu ana ci gaba da tantance wadanda lamarin ya shafa.

Des combattants de groupes d'autodéfense civils, à Ouagadougou, en mars 2020.
Des combattants de groupes d'autodéfense civils, à Ouagadougou, en mars 2020. © AP - Sam Mednick

Bayanai dai sun ce, ‘yan ta’adda sun yi wa ‘yan sa kan kwanton Bauna ne, a lokacin da suke yi wa wani ayarin ‘yan kasuwa rakiya a kusa da Ouahigouya, wani gari da ba shi da nisa da kan iyakar Mali.

Harin na baya bayan nan dai shi ne mafi muni a Burkina Faso, tun tsakiyar watan Nuwamba inda aka kashe mutane 57 da suka hada da Jandarmomi 53.

Kamar makwaftanta da suka hada da Mali da Jamhuriyar Nijar, Burkina Faso na fama da tashe-tashen hankula tun shekara ta 2015, sakamakon kungiyoyin mayaka masu ikirarin jihadi, wadanda suka yi wa kungiyar Al-Qaeda da IS mubaya’a.

Hare-haren mayakan dai ya yi sanadin mutuwar mutane akalla dubu 2,000 tare da raba wasu miliyan 1.4 da muhallansu a kasar ta Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.