Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo - Ta'addanci

Dan kunar bakin wake ya kashe mutane 5 a Jamhuriyar Congo

Wani dan kunar bakin wake ya kashe akalla mutane 5 a wani wurin biki cikin dare a birnin Beni da ke Lardin Kivu ta Arewa a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Yadda harin kunar bakin wake ya tarwatsa wajen biki a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo.
Yadda harin kunar bakin wake ya tarwatsa wajen biki a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo. © AFP / Seros MUYISA
Talla

Tuni dai Jami'ai suka dora alhakin harin na ranar Asabar akan kungiyar Allied Democratic Forces ADF, daya daga cikin kungiyoyin masu dauke da makamai a yankin, wadda kungiyar IS ta bayyana a matsayin reshen ta a tsakiyar Afirka.

Sanarwar da jami'an gwamnatin Jamhuriyar ta Congo suka fitar, ta ce harin kunar bakin waken ya jikkata wasu mutane 13, zalika sun bayyana adadin wadanda suka mutu a matsayin na wucin gadi.

Wasu shaidun gani da ido sun ce fiye da mutane 30 ne suke bikin ranar Kirsimeti a lokacin da bam din ya tarwatse a gabashin birnin na Beni.

A ranar 27 ga watan Yuni a dai garin na Beni, wani bam da aka dasa na gida a cocin Katolika ya jikkata mata biyu, rana guda bayan da wani mutum ya mutu lokacin da bam din da yake dauke da shi ya tarwatse.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.