Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

'Yan bindiga sun kashe mutane 14 a gabashin Jamhuriyar Congo

Fararen hula akalla 14 ne aka kashe a arewa maso gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo a jiya Juma'a lokacin da wasu kungiyoyin mayaka biyu suka kai wa kauyensu hari.

Wani yanki na Lardin Kivu dake gabashin Jamhuriyar Congo
Wani yanki na Lardin Kivu dake gabashin Jamhuriyar Congo RFI/Sonia Rolley
Talla

Masu sa ido sun ce, maharani sun kai farmakin ne kan kauyen Gina dake lardin Ituri, inda suka shafe tsawon sa’o’i bakwai suna cin karensu babu babbaka kafin daga bisani sojoji su sake kwace iko da yankin.

Ituri na daya daga cikin larduna uku na gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da ke fama da kungiyoyin masu dauke da makamai.

Lardi mai arzikin Zinari dai na da dadadden tarihin rikicin kabilanci tsakanin manoma da makiyaya.

An gwabza fada tsakanin ‘yan kabilar Hema da Lendu tsakanin 1999 zuwa 2003, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, kafin dakarun wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Turai su kawo karshen rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.