Isa ga babban shafi
Congo-ADF

Mayakan ADF sun hallaka fararen hula 50 a Jamhuriyyar Congo

Akalla mutane 50 suka mutu a wasu tagwayen hare-hare da mahukuntan Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ke zargin mayakan kungiyar ADF mai biyayya ga kungiyar IS da kaddamarwa a wasu kauyukan lardin Kivu.

Wasu Sojin Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.
Wasu Sojin Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo. © REUTERS - OLIVIA ACLAND
Talla

Majiyoyin tsaro a Congo sun dora alhakin farmakin na tsakaddare kan kungiyar ta ADF wadda ta samo asali daga makwabciyar kasar Uganda kuma yanke ta ke biyayya ga babbar kungiyar ta’addanci ta Duniya IS.

Cikin watanni 18 da suka gabata, kungiyar ta ADF ta tsananta kai makamantan hare-haren na tsakaddare tare da kisan tarin fararen hula.

Wata majiyar ta daban a Boga ta ce mayakan na ADF sun kuma farmaki wani sansanin mutanen da rikici ya raba da muhallansu da ke yankin tare da kashe mutum 36, ko da ya ke mahukuntan kasar ba su kai ga tabbatar da batun ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.