Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo

'Yan tawaye sun kona fararen hula 19 har lahira a Congo

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun ce  Fararen hula 19 ne ‘yan tawayen Uganda suka daddatse tare da kone su har lahira.

Map of DR Congo locating Goma
Map of DR Congo locating Goma AFP
Talla

An tsinci gawarwaki 14 a ranar Asabar, kwana guda bayan aukuwar lamarin, kamar yanda kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito.

Wani basaraken yanki ya ce jami’an kungiyar agaji ta Red Cross ne suka gano gawarwakin a yayin da suka shiga daji don neman wadanda suka bace a yayin harin da aka kai kauyen Kasanzi da ke yankin Beni a arewacin Kivu.

Beni  na tsakiyar yankin da kungiyar ‘yan tawaye ta Allied Democratic Forces (ADF), mai nasaba da ISIS ta ke kai munanan hare hare duk matakin dokar ta baci da shugaba Felix Tshisekedi ya dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.