Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Ana binciken tsohon shugaban DR Congo kan zargin almubazzaranci

Hukumomin Jamhuriyar Demokradiyar Kwango na binciken kan wani rahoton da ya bankado tsohon shugaban kasar Joseph Kabila da iyalansa da yin sama da fadi da kudaden gwamnati da suka kai dalar Amurka miliyan 138.

Tsohon shugaban Jamhuriyar Demokradiyar Congo, Jospeh Kabila.
Tsohon shugaban Jamhuriyar Demokradiyar Congo, Jospeh Kabila. © RFI
Talla

Binciken da wata kungiyar kafafen yada labarai masu zaman kasansu ta duniya da ke yaki da cin hanci da rashawa ya yi matukar tada hankali a kasar dake tsakiyar Afirka.

Miliyoyin bayanai da suka tattara sun zargi Kabila, wanda ya mulki Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango daga shekarar 2001 zuwa 2019 bayan ya karbi mulki daga hannun mahaifinsa da akayiwa kissan gilla, da cewar ya yi almubazzaranci tsakanin shekarar 2013 da 2018.

Mai magana da yawun gwamnati Patrick Muyaya ya ce tun ranar Litinin ministan shari'a "ya bukaci mai gabatar da kara da ya fara gudanar da binciken  a ranar 20 ga watan Nuwamba," kwana daya bayan da aka fara wallafa tonon sililin.

Cikin umurnin da Ministan ya baiwa mai gabatar da karar gwamnatin kasar, har da gurfanar da wadanda ake zargi da badakalar bayaga binciken.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.