Isa ga babban shafi
DR Congo

Joseph Kabila ya kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya

Shugaban kasar Jamhuriyyar Congo, Joseph Kabila ya sanar da kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya, wadda kuma mafi yawan jami’an da ke ciki na hannun damansa ne.

Shugaban kasar DR Congo Joseph Kabila
Shugaban kasar DR Congo Joseph Kabila REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Matakin da ‘yan adawa suka bayyana a matsayin cin amanar matsayar da aka cim-ma a baya, tare da bukatar nan ta ke Kabila ya janye sanarwar.

Tun a shekara ta 2001 ne dai Kabila ya cim-ma yarjejeniya da gamayyar jam’iyyun adawar kasar, wadda ta ba shi damar ci gaba da jan ragamar mulkin kasar duk da karewar wa’adinsa a waccana lokaci, amma fa da sharadin cewa zai bada damar shirya zaben shugabancin kasar a karshen shekarar da muke ciki.

To sai dai tattaunawa tsakanin Gwamnatin Kabila da ‘yan dawa kan yadda za’a aiwatar da yarjejeniyar da aka cim-ma ta rushe a watan Maris din da ya gabata bayanda, Kabila ya ki amincewa da Framinsitan da bangaren ‘yan adawa suka gabatar don kafa gwamnatin hadaka.

A gefe guda kuma ambata Bruno Tshibala a matsayin sabon Firaminsta wanda a ba ya ya ke bangaren ‘yan adawa, ya nuna yadda Joseph kabila ya samu nasarar sauya ra’ayin da dama daga cikin ‘yan dawar zuwa bangarensa.

Tuni dai gamayyar jam’iyyun dawar Jamhuriyyar Congon suka yi watsi da sabbin nade naden tare da bukatar Kabila ya sauya zuwa abinda yarjejeniyar da aka cim-ma a watan Disambar Bara ta kunsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.