Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo

An gaza kawo karshen rikicin siyasar Jamhuriyar Congo

An gaza cinma matsaya a tattaunawar da aka yi a Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, tsakanin wakilan Jam’iyya mai mulki dana ‘yan adawa, domin kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Shugaban kasar Jamhuriyyar Congo Joseph Kabila.
Shugaban kasar Jamhuriyyar Congo Joseph Kabila. REUTERS/Tiksa Negeri/File Photo
Talla

A ranar Litinin mai zuwa wa’adin Shugaban kasar, Joseph Kabila zai kare, yayinda a gefe guda, yake neman yin tazarce, abinda ‘yan adawa suka ce ba zasu lamunta ba.

Rahotanni sun ce yanzu haka ana zaman dar dar a wasu sassan kasar, inda jami’an ‘yan sanda ke kafa shingayen bincike a wasu titunan babban birnin kasar Kinshasa, yayinda wasu jami’an tsaron ke sintiri yankunan da ke kusa da fadar gwamnati.

Jami’an Diflomasiya musamman na kasashen turai sun bukaci jama’arsu da ke kasar ta Jamhuriyar Congo su fice daga kasar, saboda fargabar barkewar rikici.

Sai dai kuma a wata zantawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na Reuters, wani jagoran ‘yan adawa, Fellix Tshisekedi ya ce ba zasu gudanar da wata zanga-zanga ba, domin kada hakan ya jefa fareren hula cikin wani hali, sai dai suna kan matsayinsu na neman saukar shugaban kasar Joseph Kabila.

Gwamnatin Kabila na cigaba da kare matsayinta na cewa bazata iya shirya gudanar da babban zaben kasar ba har sai a shekara ta 2018,saboda dalilan rashin kudi.

A wani cigaban kuma, wakilai sun ce za’a cigaba da tattaunawa a ranar Laraba mai zuwa, bayan dawowar limaman darikar Katolika da ke shiga tsakani daga birnin Rome.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.