DR Congo
Rikicin kabilanci a Jamhuriyar Congo ya hallaka mutane 34
Wata kungiyar ‘yan ta’adda daga kabilar Nande ta kashe fararen hula 34 ‘yan kabilar Hutu a wani tashin hankali a tsakanin bangarorin biyu a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
Wallafawa ranar:
Talla
Shugaban mulkin Yankin Lubero dake Arewacin Kivu, Joy Bokole ya ce maharan sun kai samamen ne a kauyen Luhanga jiya da asuba dauke da bindigogi da kuma adduna.
Rikicin kabilanci da kuma kokarin mallakar ma’adinai na daga cikin abinda ke raba kan kabilun kasar wadanda ke fada da muggan makamai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu