Isa ga babban shafi
DRC

MDD ta bukaci Joseph Kabila ya bar Mulki

Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci Shugaban kasar Jamhuriyar Dimokradiyar Congo Joseph Kabila ya sauka daga mulki kamar yadda aka yi da shi cikin yarjejeniyar shekara ta 2016.

Antonio Guterres
Antonio Guterres REUTERS/Mike Segar
Talla

Kalaman Guterres na zuwa ne bayan da aka sami kazamin boren da jami’an tsaro suka kashe masu zanga-zangar kyamar Gwamnatin Kabila akalla mutum 7 da jikkata wasu 120.

Mista Guterres ya bukaci Gwamnatin Congo da jami’an tsaro sun mutunta doka da nesanta kansu daga shiga hakkin al’ummar kasar na ‘yancin fadin albarkacin baki da zaman lafiya.

Tun a ranar lahadin da ta gabata mutanen kasar da dama ke addu’o’in ganin Joseph Kabila ya sauka daga mulki.

Kasar Congo da ke da arzikin albarkatun kasa amma ke fama da rashin kwanciyar hankali, ba a taba samun tsarin mika mulki cikin kwanciyar hankalin ba tun samun ‘yanci kai daga Belgium a shekara ta 1960.

Shugaba Kabila da ya gaji mulki daga mahaifinsa da aka kashe Laurent Kabila a shekara ta 2001, kuma ke ci gaba da nuna turjiyar sauka daga mulki ya ce sai a karshen 2018 za a gudanar da wani sabon zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.