Isa ga babban shafi

Gwamnatin Jamhuriyar Congo ta bada umarnin katse layukan sadarwa

Gwamnatin Jamhuriyar Congo, ta bai wa kamfanonin sadarwa umarnin katse layukan waya da na Intanet a baki dayan kasar, yayinda ‘yan adawa ke shirin fara gagarumar zanga-zanga.

Daruruwan masu zanga-zangar neman shugaban kasar Jamhuriyar Congo Joseph Kabila ya sauka daga mukaminsa.
Daruruwan masu zanga-zangar neman shugaban kasar Jamhuriyar Congo Joseph Kabila ya sauka daga mukaminsa. AFP
Talla

Wani lokaci a ranar yau Lahadi, ‘yan adawar suka bukaci ‘yan kasar su yi dandazo, domin tilastawa Joseph Kabila janye aniyarsa, ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, domin bashi damar sake neman shugabanci karo na uku.

Zalika ‘yan adawar na fatan samun nasarar tilastawa Kabila sakin daruruwan ‘yan adawar da ya garkame a gidan yari.

Tun a watan Disambar shekarar da ta gabata wa’adin shugabancin Joseph Kabila ya kare, sai dai gwamnatinsa, ta ci gaba da jan kafa wajen shirya sabon zabe, bisa dalilan da take dagantawa da rashin isassun kudaden da zai bata damar shirya zaben kamar yadda ya kamata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.