Jami'an tsaro na kashe masu zanga-zanga a Congo
Mutane 8 aka kashe yayin da aka raunata sama da 100 a zanga-zangar da ake yi na neman shugaban ƙasar Congo Joseph Kabila da ya sauka daga kan mulki.
Wallafawa ranar:
Akasarin masu zanga-zangar kiristoci ne mabiya ɗariƙar katolika waɗanda suka taru a majami’u da ke faɗin ƙasar domin gangamin neman shugaban ya kauce daga mulki.
Wakilin kamfanin dillancin labaru na Faransa ya ce, ya gani da idonsa yadda sojoji suka harbi wani mutum a ƙirji lokacin da suka bude wuta a kan masu zanga-zanga.
A wani yanki na Kinshasa babban birnin ƙasar, an yi amfani da barkono mai sa hawaye domin tarwatsa mutane, sannan aka damƙe masu jagorantar zanga-zangar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu