Isa ga babban shafi
Burundi

Amurka ta janye takunkumin da ta kakaba wa Burundi

Gwamnatin Amurka ta cire takunkumin da ta kakaba wa Burundi shekaru shida da suka gabata, bisa la’akari da zaben da aka yi, da kawo karshen tashin hankali, da kuma sauye-sauyen da shugaba Evariste Ndayishimiye ya yi.

 Evariste Ndayishimiye, shugaban Burundi.
Evariste Ndayishimiye, shugaban Burundi. TCHANDROU NITANGA AFP
Talla

Shugaba Joe Biden ya janye takunkumin da aka kakaba wa mutane 11 a kasar dake tsakiyar Afirka, galibi jami'an soji da na tsaro ciki har da ministan tsaro na gwamnati Alain Guillaume Bunyoni, wanda shi ne na biyu a gwamnati.

Halin da ake ciki a Burundi ya canza sosai sakamakon abubuwan da suka faru a cikin shekarar da ta gabata, ciki har da mika mulki bayan zabe a shekarar 2020, da raguwar tashe-tashen hankula, da kuma kokarin Shugaba Ndayishimiye na yin garambawul.

Burundi ta fada cikin tashin hankali a cikin watan Afrilun 2015, bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya kaddamar da yunkurin neman wa'adi na uku a jere, duk kuwa da damuwa kan halaccin matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.