Isa ga babban shafi
Burundi

Sabon shugaban Burundi ya sha rantsuwar fara aiki

Sabon shugaban Burundi Evariste Ndayashimiye ya sha rantuwar kama aiki a wani kayataccen biki da aka gudanar a babban birnin kasar, inda ya karbi ragamar mulki a daidai lokacin da kasar ke fama da jerin matsaloli.

Sabon shugaban Burundi Évariste Ndayishimiye.
Sabon shugaban Burundi Évariste Ndayishimiye. Tchandrou NITANGA / AFP
Talla

A cikin watan Mayun da ya gabata ne aka zabi Ndayishimiye, inda aka shirya rantsar da shi a cikin watan Agusta, amma aka matso da ranar rantsuwar baya sakamakon mutuwar farar-daya da ta dauke tsohon shugaban kasar Pierre Nkurunziza.

A yayin shan rantsuwar a yau, Ndayishimiye mai shekaru 52 ya lashi takobin sadaukar da duk karfinsa wajen kare muradun kasar Burundi tare da hada kan al’ummar kasar da kuma tabbatar da zaman lafiya da adalci a cewarsa.

Jim kadan da sanya hannu kan alkawuran da shugaban ya dauka a gaban alkalan kotun tsarin mulkin kasar, an harba bindiga har sau 21 a matsayin karramawa a gare shi.

Kazalika shugaban ya kekkewaya filin wasan da aka gudanar da wannan biki wanda kuma ya cika makil da al’ummar kasar da akasarinsu suka yi shiga iri guda.

Duk da cewa, an tilasta wa baki wanke hannayensu kafin shiga filin wasan, amma kalilan daga cikin manyan baki ne suka sanya kyallen rufa baki da hanci,, kuma ba a mutunta tsarin nesa nesa da juna ba.

Sai dai babu daya daga cikin shugabannin kasashen duniya da ya halarci bikin rantsuwar, amma jami’an diflomasiya da wakilan kungiyoyin kasa da kasa sun hallara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.