Isa ga babban shafi
Mozambique

Sojojin Rwanda za su ci gaba da yakar 'yan ta'adda a Mozambique - Kagame

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, ya ce dakarun kasar sa za su ci gaba da tallafawa sojojin Mozambique wajen yakar ‘yan ta’addan da suka addabi wasu yankunan arewacin kasar.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame.
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame. REUTERS - JEAN BIZIMANA
Talla

Kagame ya bayyana haka ne, jim kadan bayan isa kasar Mozambique a ranar Juma’a, inda ya aike da sojoji kimanin dubu 1 domin taimakawa jami’an tsaron kasar wajen murkushe mayaka masu ikirarin jihadi.

Hare-haren wata kungiya mai dauke da makamai da aka fi sani da suna al-Shabab, na ci gaba da karuwa a lardin Cabo Delgado da ke Mozambique ne tun daga watan Oktoba na shekarar 2017, lamarin da yayi sanadin kashe mutane sama da dubu 3 da 306, tare da raba wasu akalla dubu 800,000 da gidajen su cikin shekaru hudun da suka gabata.

A watan Yuli Rwanda ta zama kasa ta farko, daga cikin kasashen Afirka da suka ba da gudunmawar sojoji ga Mozambique, don kawo karshen tashin hankalin na lardin Cabo Delgado mai arzikin iskar gas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.