Isa ga babban shafi
Afirka ta Kudu

Tarzomar Afrika ta Kudu ta lakume rayukan mutane 75

Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a Afirka ta Kudu ya kai 75, sakamakon tarzomar magoya bayan tsohon shugaban kasar Jacob Zuma dake neman sakinsa daga kurkuku.

Yadda masu tarzoma suka ragargaza wasu gine-gine a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu.
Yadda masu tarzoma suka ragargaza wasu gine-gine a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu. AP - Yeshiel Panchia
Talla

Magajin garin yankin KwaZulu-Natal Sihle Zikalala ya shaidawa taron manema labarai a yau cewar yanzu haka adadin mutanen da suka mutu a tashin hankalin da ya barke ya kai 26, kwana guda bayan tabbatar da mutuwar wasu mutanen 6 a lardin Gauteng.

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana tarzomar da ta barke a Johannesburg da kuma lardin KwaZulu-Natal biyo bayan kama Jacob Zuma a matsayin mafi muni da aka taba gani tun bayan kawo karshen mulkin wariya a kasar.

Ramaphosa wanda ke gabatar da jawabi a yammacin jiya, ya ce wannan tarzoma ce da ba ta da alaka siyasa, inda ya bayar da umurnin tura sojoji don kawo karshen kone-kone da kuma wawashe dukiyoyin jama’a da aka share tsawon kwanaki ana yi.

A halin da ake ciki Jami’an tsaro sun tabbatar da mutuwar mutane 32 yayin da aka kama wasu sama da 500.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.