Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu - Jacob Zuma

Zuma ya sake musanta aikata almundahana a kwangilar cinikin makamai

Tsohon shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma, ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa da aikawa da suka hada da cin hanci da rashawa, da kuma karkatar da makudan kudade lokacin da ya jagoranci wata kwangilar sayen makamai a shekarar 1999, zamanin da yake rike da mukamin mataimakin shugaban kasar Afrika ta Kudun.

Jacob Zuma, tsohon shugaban Afrika ta Kudu.
Jacob Zuma, tsohon shugaban Afrika ta Kudu. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da a gaban kotu Zuma ke musanta laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa ba, wadanda ya bayyana a matsayin makircin siyasar da masu adawa da shi suka kulla domin bata masa suna.

Tsohon shugaban Afrika ta Kudun dai na fuskantar tuhumar karbar toshiyar bakin dala dubu 34 duk shekara daga wani kamfanin kera makamai na Faransa mai suna Thales, domin baiwa kamfanin kariya daga binciken almundahanar da aka tafka yayin kwangilar cinikin makaman dala biliyan 2 da ta gudana tsakanin kamfanin na Thales da gwamnatin Afrika ta kudu.

Baya ga fuskantar tuhuma kan badakalar cinikin makaman na 1999, tsohon shugaba Jacob Zuma na fuskantar wasu tuhume-tuhumen kan aikata laifukan Rashawa a zamanin da ya shugabanci Afrika ta Kudu daga 2009 zuwa 2018.

Lauyoyin Zuma dai na neman kotu tayi watsi da tuhume-tuhumen da ake yi masa, yayin da lauyoyin gwamnati suka nemi karin lokaci zuwa 19 ga watan Yuli, domin tattara karin shaidu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.