Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

ANC ta gaza wajen yaki da rashawa a Afrika ta Kudu- Ramaphosa

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce lallai jami’iyyarsa ta ANC mai mulki ta gaza wajen yaki da rashawa a karkashin tsohon shugaba Jacob Zuma.

Shugaban Afrikan ta kudu Cyril Ramaphosa.
Shugaban Afrikan ta kudu Cyril Ramaphosa. © Lulama Zenzile/Die Burger/Gallo Images via Getty Images
Talla

A yayin da ya bayyana a gaban kotu ta musamman da ke bincike kan zargin rashawa da ake wa tsohon shugaba Jacob Zuma, Ramaphosa ya ce rashawa ta yi wa dokar kasar karan tsaye.

Ramaphosa, shugaba mai ci na farko da ya fito a matsayin shaida a irin wannan bincike, ya bayyana ne a matsayinsa na shugaban jam’iyyar ANC  na kasa.

Gwamman ministoci masu ci, da tsaffin ministoci, da zababbun shugabanni, ‘yan kasuwa da manyan ma’aikatan gwamnati da dama sun bayyana a gaban wannan kotu.

Badakalar da ta  janyo wannan bin ba’asi dai ita ce ta sanannen iyalan Gupta, wadanda suka yi ta samun dimbin kwangiloli daga kamfanonin gwamnatin kasar, inda ma har aka zargin cewa su na iya zaben wanda su ke so ya rike mukamin minista.

Sau daya Zuma wanda ake zargi da taimaka wa ayyukan rashawa ya taba bayyana a gaban wannan kotu ta musamman a shekarar 2019, kuma tun a lokacin ya ki bada wata shaida, yana mai zargin katsalandan daga gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.