Isa ga babban shafi
Zuma-Afrika ta kudu

Jacob Zuma ya mika kansa ga 'Yan sandan Afrika ta Kudu

Tsohon Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya mika kansa ga jami’an tsaro, wadanda suka tasa keyarsa zuwa gidan yari a cikin daren jiya.

Tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma.
Tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma. Emmanuel Croset AFP/Archivos
Talla

Zuma ya bar gidansa da ke Nkandla a yankin KwaZulu-Natal ne mintuna 30 kafin karewar wa’adin da aka ba shi na ya je ya fara zaman kurkukun watanni 15 saboda samun sa da laifin rena umurnin kotu.

Da farko dai tsohon shugaban kasar ta Afrika ta Kudu, ya ce ba zai taba mika kansa ga jami’an tsaro ba, yayin da dimbin magoya bayansa suka yi cincirindo a harabar gidansa wasu dauke da makamai don hana jami’an tsaro kama shi.

To sai dai yayin da ya rage mintuna 30 wa’adin kwanaki 5 da kotun ta ba shi don mika kansa ga ‘yan sanda ne sai aka ga wani ayarin motoci kusan 10 ya bar gidan da ke KwaZulu-Natal, kafin daga bisani gidauniyar tsohon shugaban ta bayyana a shafinta na Twitter cewa Zuma mai shekaru 79 a duniya ya shiga hannun jami’’an tsaro.

Ita mai dai ma’iakatar ‘yan sandan kasar ta tabbatar da wannan labari, yayin da a halin yanzu hankula suka karkata zuwa ga Kotun Tsarin Mulkin kasar wadda za ta sake yin zama don duba yiyuwar sassauta hukuncin da ta yanke wa Jacob Zuma a ranar 12 ga wannan wata na yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.