Isa ga babban shafi
AFIRKA TA KUDU

Magoya bayan Zuma sun ce ba zai je gidan yari ba

Daruruwan magoya bayan tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma sun yi gangami a kofar gidan sa dake Nkandla domin nuna masa goyan bayan su dangane da shirin tasa keyar sa zuwa gidan yari kamar yadda kotu ta bada umurni.

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma
Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma © REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Mai shari’a Sisi Khampepe ta kotun kolin kasar a hukuncin karar da aka gabatar mata akan kin mutunta umurnin kotu dangane da tuhumar da ake yiwa tsohon shugaban na zargin cin hanci da rashawa ta bukaci tasa keyar Zuma gidan yari na watanni 15 saboda abinda ta kira karan tsayen da yake yiwa bangaren shari’a a matsayin sa na tsohon shugaban kasa.

Magoya bayan Zuma wadanda akasarin su suka fito daga bangaren dakarun ‘yayan Jam’iyyar ANC da ake kira ’Umkhonto Wesizwe’ sun kwashe kwanaki suna zaman dirshe a kofar gidan sa dake Yankin KwaZulu-Natal domin bayyanawa duniya goyan bayan sa da suke yi.

Jacob Zuma yayin bikin ANC lokacin da yake mulki
Jacob Zuma yayin bikin ANC lokacin da yake mulki (Photo : Reuters)

Mutanen sanye da fatar damisa da gashin jimina kuma rike da kibiya da garkuwa kamar yadda aka saba ganin Yan kabilar Zulu sun yi tattaki a titunan Nkandla inda suke rera wakokin kambama Zuma.

Mata daga cikin su kuwa na tikar rawa ne sanye da sarkoki da daurin kai amma kuma sun bar nonon su a bude suna kuma rera waka.

Magoya bayan Jacob Zuma a Afirka ta Kudu
Magoya bayan Jacob Zuma a Afirka ta Kudu © (Photo by Emmanuel Croset / AFP)

Wata daga cikin su ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar ta je wurin ne saboda kaunar da take yiwa tsohon shugaban wanda ya samar musu da wutar lantarki kuma a lokacin sa babu wanda aka dakile a gida, aka hana zirga zirga kamar yadda ake gani yanzu.

Magoya bayan tsohon shugaban sun yi barazanar cewar za’a samu tashin hankali da kuma rashin zaman lafiya muddin aka kama Jacob Zuma dan kai shi gidan yari, yayin da suka sha alwashin kare shi.

Domin kaucewa tashin hankali, Jam’iyyar ANC ta soke taron Majalisar zartarwar ta da ta shirya gudanarwa a karshen wannan mako.

Rahotanni sun ce tawagar manyan jami’an Jam’iyyar ANC cikin su harda Sakataren ta dake Yankin Mdumiseni Ntuli na ta ziyarar tsohon shugaban a gidan sa.

Bisa ka’ida idan Zuma yaki gabatar da kan sa a gidan yari nan da gobe lahadi, kotu zata baiwa Yan Sanda umarnin kwanaki 3 na kama shi domin kai shi inda zai yi zaman cin zarka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.