Isa ga babban shafi
AFIRKA TA KUDU

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu Zuma yace ba zai je gidan yari ba

Tsohon Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya shaidawa daruruwan magoya bayan sa da suka yi cincirindo a kofar gidan sa cewar an take masa hakkokin sa a daidai lokacin da wa’adin kotu na ganin ya gabatar da kan sa a gidan yari ke cika yau lahadi, inda yake cewa ba zai gabatar da kan sa ba.

Tsohon shugaban kasa Jacob Zuma
Tsohon shugaban kasa Jacob Zuma PHILL MAGAKOE POOL/AFP/Archivos
Talla

Zuma yace alkalan kotun kasar sun take masa hakkokin sa wajen yanke masa hukuncin tasa keyar sa zuwa gidan yari na watanni 15 saboda kin bada shaida a gaban kwamitin dake gudanar da bincike akan zargin cin hanci da rashawa da ake masa.

Magoya bayan tsohon shugaban sun sha alwashin jefa Afirka ta kudu cikin rudani muddin aka jefa Zuma gidan yari kamar yadda kotu ta bada umurni.

Yau lahadi wa’adin kwanaki 5 da aka baiwa Zuma ya gabatar da kan sa a gidan yari ke cika, amma ya zuwa wannan lokaci babu alamar cewar zai mutunta umurnin.

Wasu daga cikin magoya bayan Jacob Zuma kusa da gidan sa
Wasu daga cikin magoya bayan Jacob Zuma kusa da gidan sa REUTERS - ROGAN WARD

A wani yunkuri na tauna tsakuwa, magoya bayan tsohon shugaban sun yi gangami a kofar gidan sa dake Nkandla a Yankin KwaZulu Natal domin hana duk wani yunkuri na tura shi gidan yari.

Yayin jawabi ga magoya bayan sa, Zuma yace yadda ya ga Yan Sanda yana mamakin yadda zasu iya kaiwa gare shi wajen kutsawa a tsakanin daruruwan mutanen da suka yi gangami a kofar gidan sa domin kama shi.

Wani mai goyan bayan sa Lindokuhle Maphalala ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, koda ministan Yan Sanda Bheki Cele yaje gidan Zuma sai dai ya fara da kama su kafin kaiwa ga tsohon shugaban.

Wasu daga cikin jama’ar dake wurin sun bukaci shugaba Cyril Ramaphosa da ya sauka daga mukamin sa, yayin da suka yi alkawarin cewar daga gobe litinin zasu hana ruwa gudu a fadin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.