Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Tarzoma ta barke a Afrika ta kudu saboda tsare Jacob Zuma

Afrika ta kudu ta sanar da girke dakaru a yankunanta biyu bayan tsanantar rikicin magoya bayan Jacob Zuma da ya kai ga arangama da jami’an tsaro tare da kisan mutane 6 baya ga barnata kadarori da kuma sace-sacen kayakin jama’a a sassan kasar ciki har da birnin Johannesburg.

Wani bangare da rikicin bukatar sakin Zuma ya shafa a birnin Johannesburg.
Wani bangare da rikicin bukatar sakin Zuma ya shafa a birnin Johannesburg. REUTERS - SIPHIWE SIBEKO
Talla

Tsanantar rikicin na zuwa a dai dai lokacin da kotun tsarin mulkin kasar ke nazarin hukuncin watanni 15 da aka yankewa Jacob Zuma bayan samunsa da laifin kin mutunta kotu lokacin da ya ki amsa gayyatar da aka yi masa don yi masa shari'a kan zargin rashawar da ya dabaibaye mulkinsa.

Sanarwar girke dakarun da gwamnatin kasar ta fitar ta ce za a samar da tsaro a yankunan biyu da rikicin ya fi tsananta ciki har da KwaZulu-Natal da kuma Gauteng da nufin shawo kan boren magoya bayan tsohon shugaban.

Tun a juma'ar makon jiya magoya bayan Jacob Zuma ke gangami tare da bukatar sakin jagoran baya ga barazanar tayar da hankalin kasar matukar aka ki amincewa da sakinsa, ko da ya ke gwamnati ta sha alwashin magance duk wata barazana daga garesu.

Tsohon shugaban mai shekaru 79 duk da zarge-zargen rashawar da ya dabaibaye shi har yanzu yana da farin jini tsakanin al'ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.